3. Sarkin Yariko kuwa ya aika wurin Rahab ya ce, “Fito da mutanen da suka zo wurinki, waɗanda suka shiga gidanki, gama sun zo ne domin su leƙi asirin ƙasar duka.”
4. Amma macen ta riga ta ɓoye mutanen nan biyu, sai ta ce, “Gaskiya ce, mutanen sun zo wurina, amma ban san ko daga ina suka zo ba,
5. da maraice kuma, sa'ad da za a rufe ƙofar garin, sai mutanen suka fita, inda suka tafi kuwa ban sani ba, ku bi su da sauri, gama za ku ci musu.”
6. Gama ta riga ta kai su bisa rufin ɗaki, ta rufe su da ƙasheshen rama waɗanda ta shimfiɗa a bisa rufin.
7. Mutanen kuwa suka tafi don su bi bayansu a hanyar Urdun har zuwa mashigai. Da fitar masu bin sawun, sai aka rufe ƙofar garin.
8. Amma kafin 'yan leƙen asirin ƙasar su kwanta, sai ta tafi wurinsu a bisa rufin ɗakin,
9. ta ce musu, “Na sani Ubangiji ya ba ku ƙasar, tsoronku kuma ya kama mu har zukatan mazaunan ƙasar duka sun narke saboda ku.