20. Amma idan kika tone al'amarin nan namu, to za mu kuɓuta daga rantsuwar da kika rantsar da mu.”
21. Sai ta ce, “Bisa ga maganarku ya zama haka.” Sa'an nan ta sallame su, suka tafi. Ta kuwa ɗaura jan kirtanin a tagar.
22. Sai suka tafi, suka shiga tsaunuka, suka yi zamansu a can kwana uku har masu bin sawun suka koma, gama masu bin sawun suka yi ta nema ko'ina a hanyar, amma ba su sami kowa ba.
23. Mutanen nan biyu suka sauko daga tsaunuka, suka haye zuwa wurin Joshuwa ɗan Nun, suka faɗa masa dukan abin da ya same su.
24. Suka kuma ce masa, “Hakika, Ubangiji ya ba da ƙasar duka a hannunmu, banda wannan kuma mazaunan ƙasar duka sun firgita saboda mu.”