11. da Gileyad, da yankin ƙasar Geshuriyawa, da Ma'akatiyawa, da dukan Dutsen Harmon, da dukan Bashan, zuwa Salka,
12. da dukan mulkin Og a Bashan, wanda ya yi sarautar Ashtarot da Edirai (Og Kaɗai ne aka bari daga cikin Refayawa). Waɗannan su ne Musa ya ci da yaƙi, ya kore su.
13. Duk da haka jama'ar Isra'ila ba su kori Geshuriyawa, da Ma'akatiyawa ba, amma suka yi zamansu tare da Isra'ilawa har wa yau.
14. Kabilar Lawiyawa ne kaɗai Musa bai ba ta gādo ba, gama hadayun ƙonawa na Ubangiji, Allah na Isra'ila, su ne gādonta, kamar yadda Ubangiji ya faɗa masa.
15. Musa ya riga ya ba Ra'ubainawa nasu gādo bisa ga iyalansu.
16. Nasu yankin ƙasar ya miƙa daga Arower wadda take a gefen kwarin Arnon, da birnin da yake tsakiyar kwarin, da dukan ƙasar tudu kusa da Medeba,
17. da Heshbon, da dukan biranenta da suke kan tudu, wato Dibon, da Bamot-ba'al, da Ba'al-mayon,
18. da Yahaza, da Kedemot, da Mefayat,
19. da Kiriyatayim, da Sibma, da Zeret-shahar da yake bisa tudun da yake cikin kwarin,