Josh 10:17-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Aka faɗa wa Joshuwa cewa, “An sami sarakunan nan biyar, sun ɓuya a kogo a Makkeda.”

18. Sai Joshuwa ya ce, “Ku mirgina manyan duwatsu, ku rufe bakin kogon, sa'an nan ku sa mutane su yi tsaronsu.

19. Amma kada ku tsaya a can, sai ku runtumi abokan gābanku, ku bugi na bayansu, kada ku bar su su shiga biranensu, gama Ubangiji Allahnku ya riga ya ba da su a hannunku.”

20. Joshuwa da jama'ar Isra'ila suka karkashe su da yawa ƙwarai, sauransu kuma da suka ragu suka shiga birane masu garu.

21. Sa'an nan dukan mutane suka koma wurin Joshuwa a sansani a Makkeda lafiya. Ba kuma mutumin da ya tsokani Isra'ilawa.

22. Sa'an nan Joshuwa ya ce, “Ku buɗe bakin kogon, ku kawo mini waɗannan sarakuna biyar da suke a kogon.”

23. Suka yi haka nan, suka kawo masa sarakunan nan biyar daga cikin kogon, wato Sarkin Urushalima, da Sarkin Hebron, da Sarkin Yarmut, da Sarkin Lakish, da Sarkin Eglon.

Josh 10