Ish 59:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Duba, ikon Ubangiji bai kasa ba, har da ba zai yi ceto ba. Shi ba kurma ba, har da ba zai ji ba.

2. Amma laifofinku suka raba tsakaninku da Allahnku. Zunubanku ne kuma suka sa ya juya daga gare ku don kada ya ji ku.

3. Gama hannuwanku sun ƙazantu da jini, yatsotsinku kuma sun ƙazantu da mugunta, leɓunanku kuma suna faɗar ƙarairayi, harsunanku kuwa suna raɗar mugunta.

4. Ba wanda yake kai ƙara ta gaskiya, ba wanda yake yanke shari'a da adalci. Kuna dogara ga shaidar ƙarya, kuna faɗar ƙarya, kuna ɗaukar ciki na ɓarna, ku haifi mugunta.

5. Kuna ƙyanƙyashe ƙwan kāsa, kuna saƙa da saƙar gizogizo. Duk wanda ya ci ƙwayayenku zai mutu, ƙwan da ya fashe zai ƙyanƙyashe kububuwa.

6. Saƙarku ba za ta yi amfani kamar tufa ba, ba za ku yi sutura da abin da kuka yi ba. Ayyukanku ayyukan mugunta ne, kuna aikata ayyukan kama-karya.

7. Kukan sheƙa a guje don ku aikata mugunta, kuna gaggawar zub da jinin marasa laifi. Tunaninku tunanin mugunta ne, lalatarwa da hallakarwa suna a manyan karaukunku.

8. Hanyar salama ba ku san ta ba. Ba adalci a hanyoyinku, kukan karkatar da hanyoyinku, ba wanda zai yi tafiya lafiya a cikinku.

Ish 59