Ish 43:5-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Kada ku ji tsoro, ina tare da ku!“Daga gabas mafi nisa, da kuma yamma mafi nisa,Zan kawo jama'arku zuwa gida.

6. Zan faɗa wa kudu su bar su su tafi,Arewa kuma kada su riƙe su a can.Bari mutanena su komo daga manisantan ƙasashe,Daga kowane sashi na duniya.

7. Su mutanena ne, na kaina,Na kuwa halicce su don su girmama ni.”

8. Allah ya ce,“Kirawo mutanena a ɗakin shari'a.Suna da idanu, amma makafi ne,Suna da kunnuwa, amma kurame ne!

9. Kirawo sauran al'umma, su zo ga shari'a.A cikin allolinsu wane zai iya faɗar abin da yake a gaba?A cikinsu wa ya yi hurci a kan abin da yake faruwa yanzu?Bari waɗannan alloli su kawo shaidunsuDon su tabbatar daidai suke,Su shaida gaskiyar maganganunsu.

10. “Ya jama'ar Isra'ila, ku ne shaiduna,Na zaɓe ku al'umma, baiwata,Domin ku san ni, ku gaskata ni,Ku kuma fahimta, ni kaɗai ne Allah.In banda ni ba wani Allah,Ba a taɓa yin wani ba,Ba kuwa za a yi ba.

11. “Ni kaɗai ne Ubangiji,Ni kaɗai ne wanda yake da ikon yin ceto.

12. Na faɗi abin da zai faruSa'an nan na zo domin taimakonku.Ba wani gunkin da ya taɓa yin haka,Ku ne shaiduna.

13. Ni ne Allah, haka kuwa nake tutur,Ba wanda zai iya tserewa daga ikona,Ba mai iya sāke abin da na riga na yi.”

14. Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Ubangiji wanda ya fanshe ku ya ce,“Domin in cece ku zan aiko sojoji gāba da Babila,Zan rushe ƙofofin birni,Sowar mutanen birnin za ta zama kuka.

15. Ni ne Ubangiji, Allahnku Mai Tsarki na Isra'ila,Ni na halicce ku, ni ne kuma sarkinku.”

16. Tuntuni Ubangiji ya shirya hanya ta cikin teku,Da turba kuma a cikin ruwa.

17. Ya bi da manyan sojoji zuwa hallaka,Sojojin karusai da na dawakai.Sun faɗi warwar, ba za su ƙara tashi ba,An hure su kamar 'yar wutar fitila!

18. Amma Ubangiji ya ce,“Kada ku maƙale wa abubuwan da suka wuce,Ko ku riƙa tunanin abin da ya faru tuntuni.

19. Ku duba abin da nake shirin yi.Yana ta faruwa ma, kuna iya ganinsa yanzu!Zan yi hanya a cikin jeji,In kuma ba ku rafuffukan ruwa a can.

20. Har da namomin jeji za su girmama ni,Diloli da jiminai za su yi yabonaSa'ad da na sa kogunan ruwa su yi gudu a hamada,Domin su ba da ruwa ga zaɓaɓɓun mutanena.

Ish 43