Ish 38:7-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Ishaya ya ce wa Hezekiya, “Ubangiji zai nuna maka alama da za ta tabbatar maka zai cika alkawarinsa.

8. Ubangiji zai komar da inuwa baya da taki goma, bisa ga ma'aunin rana na sarki Ahaz.” Inuwa kuwa ta koma da baya daga fuskar rana har mataki goma.

9. Bayan da Hezekiya ya warke daga rashin lafiyarsa, sai ya rubuta wannan waƙar yabo.

10. Na zaci a gaɓar ƙarfinaZan tafi lahira,Ba zan ƙara rayuwa ba.

11. Na zaci ba zan ƙara ganin Ubangiji baA wannan duniya ta masu rai,Ko kuwa in ga wani mutum mai rai.

12. An datse raina, ya ƙare,Kamar alfarwar da aka kwance,Kamar saƙar da aka yanke,Na zaci Allah zai kashe ni.

13. Dare farai na yi ta kuka saboda azaba,Sai ka ce zaki yake kakkarya ƙasusuwana.Na zaci Allah zai kashe ni.

14. Muryata ƙarama ce, ba kuma ƙarfi,Na kuwa yi kuka kamar kurciya,Idanuna sun gaji saboda duban sama.Ya Ubangiji, ka cece ni daga dukan wannan wahala.

15. Me zan iya faɗa? Ubangiji ne ya yi wannan.Ina da ɓacin zuciya, ba na iya barci.

16. Ya Ubangiji, zan bi ka, kai kaɗai.Ka warkar da ni, ka bar ni da rai.

17. Ɓacin zuciyata zai juya ya zama salama.Ka ceci raina daga dukan hatsari,Ka gafarta dukan zunubaina.

Ish 38