11. Na zaci ba zan ƙara ganin Ubangiji baA wannan duniya ta masu rai,Ko kuwa in ga wani mutum mai rai.
12. An datse raina, ya ƙare,Kamar alfarwar da aka kwance,Kamar saƙar da aka yanke,Na zaci Allah zai kashe ni.
13. Dare farai na yi ta kuka saboda azaba,Sai ka ce zaki yake kakkarya ƙasusuwana.Na zaci Allah zai kashe ni.
14. Muryata ƙarama ce, ba kuma ƙarfi,Na kuwa yi kuka kamar kurciya,Idanuna sun gaji saboda duban sama.Ya Ubangiji, ka cece ni daga dukan wannan wahala.
15. Me zan iya faɗa? Ubangiji ne ya yi wannan.Ina da ɓacin zuciya, ba na iya barci.
16. Ya Ubangiji, zan bi ka, kai kaɗai.Ka warkar da ni, ka bar ni da rai.
17. Ɓacin zuciyata zai juya ya zama salama.Ka ceci raina daga dukan hatsari,Ka gafarta dukan zunubaina.
18. Ba wanda yake yabonka a lahira,Matattu ba za su iya dogara ga amincinka ba.
19. Masu rai ne suke yabonka,Kamar yadda nake yabonka yanzu.Iyaye za su faɗa wa 'ya'yansu irin amincinka.
20. Ya Ubangiji, ka riga ka warkar da ni!Za mu kaɗa garayu mu kuma raira waƙar yabo,Za mu raira yabo cikin Haikalinka muddin ranmu.
21. Haka ya faru bayan da Ishaya ya faɗa wa sarki ya sa curin da aka yi da 'ya'yan ɓaure a kan marurun, ya kuwa warke.
22. Sarki Hezekiya ya riga ya yi tambaya ya ce, “Me zai zama alama ta cewa zan iya zuwa Haikali?”