13. A maimakon haka sai kuka yi dariya, kuka yi biki. Kuka yanka tumaki da shanu don ku ci, kuka sha ruwan inabi. Kuka ce, “Gara mu ci mu sha! Gobe za mu mutu.”
14. Ubangiji Mai Runduna ya ce mini, “Ko kusa ba za a gafarta musu wannan mugunta ba muddin ransu. Ni, Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”
15. Ubangiji Mai Runduna ya faɗa mini in tafi wurin Shebna, mai hidimar iyalin gidan sarki, in ce masa,
16. “Kana tsammani kai wane ne? Wa ya ba ka 'yancin sassaƙa wa kanka kabari a jikin duwatsu?
17. Yana yiwuwa kai wani abu ne, amma Ubangiji zai ɗauke ka, ya jefar.
18. Zai dunƙule ka kamar ƙwallo ya jefa ka a cikin ƙasar da ta fi girma. A can za ka mutu a kusa da karusan da kake fāriya da su. Abin kunya kake a gidan maigidanka!
19. Ubangiji zai fisshe ka daga maƙaminka, ya ƙasƙantar da kai daga babban matsayinka!”
20. Ubangiji ya ce wa Shebna, “Idan haka ya faru zan aika wa bawana Eliyakim ɗan Hilkiya.
21. Zan sa masa tufafin sarautarka, in ɗaura masa ɗamara, in kuma ba shi dukan ikon da kake da shi. Zai zama kamar uba ga jama'ar Urushalima da na Yahuza.
22. Zan sa shi ya zama sarki mai cikakken iko, na zuriyar Dawuda. Mabuɗan fāda suna hannunsa, abin da ya buɗe, ba mai ikon rufewa. Abin da ya rufe kuwa ba mai ikon buɗewa.
23. Zan kafa shi da ƙarfi a wurin kamar turke, zai kuwa zama sanadin daraja ga dukan iyalinsa.
24. “Amma dukan 'yan'uwansa da masu dogara gare shi za su zama nawaya a gare shi. Za su rataya gare shi kamar tukwane da ƙoren da aka sa a ragaya!