Irm 6:18-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. “Don haka, ku ji, ya ku al'ummai,Ku sani, ku taron jama'a,Don ku san abin da zai same ku.

19. Ki ji, ya ke duniya,Ga shi, ina kawo masifa a kanwannan jama'a,Sakayyar ƙulle-ƙullensu,Don ba su kula da maganata ba,Sun ƙi dokokina.

20. Da wane nufi kuke kawo mini turaredaga Sheba,Ko raken da kuke kawowa dagaƙasa mai nisa?Ba zan karɓi hadayunku na ƙonawaba,Ba kuwa zan ji daɗin sadakokinkuba.

21. Don haka, ni Ubangiji na ce,Zan sa abin tuntuɓe a gaban wannanjama'a,Za su kuwa yi tuntuɓe, su fāɗi.Iyaye tare da 'ya'yansu, damaƙwabci,Do abokansu za su lalace.”

22. Haka Ubangiji ya ce,“Ga shi, jama'a tana fitowa dagaƙasar arewa.Babbar al'umma ce,Ta yunƙuro tun daga manisantanwurare na duniya.

23. Suna riƙe da baka da māshi,Mugaye ne marasa tausayi,Motsinsu kamar ƙugin teku ne.Suna haye a kan dawakai,A jere kamar wanda ya yi shirinyaƙiGāba da ke, ya 'yar Sihiyona.”

24. Mutanen Urushalima sun ce,“Mun ji labarin yaƙin,Hannuwanmu suka yi rauni.Azaba ta kama mu,Ciwo irin na mai naƙuda.

25. Kada ku fita zuwa gona,Kada kuma ku yi yawo a kanhanya,Gama abokin gāba yana da takobi,Razana a kowane sashi.”

26. “Ya mutanena, ku sa tufafin makoki,Ku yi birgima cikin toka,Ku yi makoki mai zafi irin wandaakan yi wa ɗa tilo,Gama mai hallakarwa zai auko mananan da nan.”

27. Ubangiji ya ce wa Irmiya,“Na maishe ka mai aunawa da maijarraba mutanenaDomin ka sani, ka aunaal'amuransu,

Irm 6