2. Sarki Zadakiya ya aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji kamar yadda Sarki Yehoyakim ya yi.
3. Al'amarin ya zama da muni ƙwarai a cikin Isra'ila da Yahuza, don haka Ubangiji ya husata har ya sa aka kai mutanen bautar talala.Zadakiya kuwa ya tayar wa Sarkin Babila.
4. A kan rana ta goma ga watan goma, a shekara ta tara ta mulkin Zadakiya, Sarkin Yahuza, sai Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya zo yaƙi da Urushalima tare da dukan sojojinsa. Suka kewaye ta da yaƙi, suka gina garu kewaye da ita.
5. An kewaye birnin da yaƙi har shekara ta goma sha ɗaya ta mulkin Zadakiya.
6. A kan rana ta tara a watan huɗu na wannan shekara, yunwa ta tsananta ƙwarai a birnin. Mutane suka rasa abin da za su ci.
7. Sai aka huda garun birnin, sojojin kuwa suka gudu, suka fita daga cikin birnin da dare ta hanyar ƙofar da take tsakanin bango biyu, kusa da gonar sarki, sa'ad da Kaldiyawan take kewaye da birnin. Sojojin suka nufi wajen Araba.
8. Amma sojojin Kaldiyawa suka runtumi sarki Zadakiya, suka ci masa a filayen Yariko. Dukan sojoji suka yashe shi.
9. Da aka kama Zadakiya, sai aka kai shi wurin Sarkin Babila a Ribla a ƙasar Hamat, a nan ne Sarkin Babila ya yanke masa shari'a.
10. Ya kuwa kashe 'ya'yan Zadakiya a idonsa. Ya kuma kashe dukan shugabannin Yahuza a Ribla.
11. Sa'an nan ya ƙwaƙule idanun Zadakiya, ya kuma sa masa ƙuƙumi, aka kai shi Babila inda aka sa shi a kurkuku har ran da ya mutu.
12. A kan rana ta goma ga watan biyar a shekara ta goma sha tara ta sarautar Nebukadnezzar, Sarkin Babila, sai Nebuzaradan shugaban matsara da kuma ɗan majalisar sarki, ya zo Urushalima.
13. Sai ya ƙone Haikalin Ubangiji, da gidan sarki, da dukan manyan gidajen da suke Urushalima.
14. Sojojin Kaldiyawa da suke tare da shugaban matsara, suka rushe dukan garun Urushalima.
15. Sa'an nan Nebuzaradan shugaban matsara ya kwashe waɗansu matalauta, da sauran mutane da aka bari a birnin, da waɗanda suka gudu zuwa wurin Sarkin Babila, da sauran masu sana'a, ya kai su bautar talala a Babila.
16. Amma ya bar waɗansu matalauta na gaske a ƙasar don su yi aiki a gonakin inabi, da sauran gonaki.
17. Kaldiyawa kuwa suka farfasa ginshiƙan tagulla, da dakalai, da babbar kwatarniya, waɗanda suke a Haikalin Ubangiji. Suka kwashe tagulla duka suka kai Babila.
18. Suka kwashe tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da hantsuka, da daruna, da tasoshin ƙona turare, da kayayyakin tagulla waɗanda ake amfani da su domin hidimar Haikali.
19. Suka kuma kwashe ƙananan kwanonin sha, da farantan wuta, da daruna, da tukwane, da alkukai, da tasoshin ƙona turare, da kwanonin miƙa hadayar sha. Duk abin da yake na zinariya da azurfa, shugaban matsara ya kwashe.
20. Tagullar da sarki Sulemanu ya yi waɗannan abubuwa da ita, wato ginshiƙai biyu, da kwatarniyar tagulla, da bijimai goma sha biyu, waɗanda suke ɗauke da kwatarniya, da dakalai, ta fi ƙarfin a auna.