Irm 51:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce,“Ga shi, zan kawo iskar ɓarna akan BabilaDa mazaunan Kaldiya.

2. Zan aika da masu casawa zuwaBabila, za su casa ta,Su bar ƙasarta kango.Za su kewaye ta a kowane sashiA wannan ranar masifa.

3. Kada ku bar maharbi ya yi harbi dabakansa,Kada kuma ya sa kayan yaƙinsa,Kada ku rage samarinta,Ku hallaka dukan sojojinta.

4. Za su fāɗi matattu a ƙasarKaldiyawa,Za a sassoke su a titunansu.”

5. Allah na Isra'ila da Yahuza,Ubangiji Mai Runduna, bai yashesu ba,Ko da yake sun yi wa Mai Tsarki naIsra'ila zunubi.

6. Ku gudu daga cikin Babila,Bari kowa ya ceci ransa,Kada a hallaka ku tare da ita,Gama a wannan lokaci Ubangiji zaisāka mata,Zai sāka mata bisa ga alhakinta.

7. Babila ta zama ƙoƙon zinariya ahannun Ubangiji,Ta sa dukan duniya ta yi maye.Ƙasashen duniya sun sha ruwaninabinta, suka haukace.

8. Farat ɗaya, Babila ta fāɗi, takakkarye,Ku yi kuka dominta!Ku samo mata magani domin azabarda take sha, watakila ta warke.

Irm 51