Zadakiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki a Urushalima shekara goma sha ɗaya. Sunan uwarsa Hamutal, 'yar Irmiya, wanda yake zaune a Libna.