Irm 5:22-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Ubangiji ya ce, “Ba za ku ji tsoronaba?Ba za ku yi rawar jiki a gabana ba?Ni ne na sa yashi ya zama iyakarteku,Tabbatacciyar iyaka, wadda ba tahayuwa,Ko da yake raƙuman ruwa za su yihauka, ba za su iya haye ta ba,Ko da suna ruri, ba za su iya wuce taba.

23. Amma mutanen nan suna da taurinzuciya, masu halin tayarwa ne,Sun rabu da ni, sun yi tafiyarsu.

24. A zuciya ba su cewa,‘Bari mu ji tsoron UbangijiAllahnmuWanda yake ba mu ruwan sama akan kari,Na kaka da na bazara,Wanda yake ba mu lokacin girbi.’

25. Laifofinku sun raba ku da waɗannanabubuwa.Zunubanku kuma sun hana kusamun alheri.

26. “Gama an sami mugaye, a cikinjama'ata,Suna kwanto kamar masu kafaashibta.Sun ɗana tarko su kama mutane.

27. Kamar kwando cike da tsuntsaye,Haka nan gidajensu suke cike da cinamana,Don haka suka zama manya, sukasami dukiya.

28. Sun yi ƙiba, sun yi bul-bul,Ba su da haram a kan aikatamugunta,Ba su yi wa marayu shari'ar adalci,don kada su taimake su.A wajen shari'a ba su bin hakkinmatalauta.

29. “Ba zan hukunta su sabodawaɗannan abubuwa ba?Ba zan ɗaukar wa kaina fansa a kanal'umma irin wannan ba?

30. “Abin banmamaki da bantsoroYa faru a ƙasar.

31. Annabawa sun yi annabcin ƙarya,Firistoci kuma sun yi mulki da ikonkansu,Mutanena kuwa suna so haka!Amma sa'ad da ƙarshe ya zo, me zaku yi?”

Irm 5