Irm 46:6-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Masu saurin gudu ba za su tsere ba,Haka nan kuma jarumi,A arewa a gefen Kogin Yufiretis,Sun yi tuntuɓe, sun fādi.

7. Wane ne wannan mai tashi kamarKogin Nilu,Kamar kogunan da ruwansu yakeambaliya?

8. Masar tana tashi kamar Nilu,Kamar kogunan da ruwansu yakeambaliya.Masar ta ce, “Zan tashi, in rufeduniya,Zan hallaka birane da mazaunacikinsu.”

9. Ku haura, ku dawakai,Ku yi sukuwar hauka, ku karusai!Bari sojoji su fito,Mutanen Habasha da Fut masuriƙon garkuwoyi,Da mutanen Lud, waɗanda suka iyariƙon baka.

10. Wannan rana ta Ubangiji, Allah MaiRunduna ce,Ranar ɗaukar fansa ce don ya ramawa maƙiyansa.Takobi zai ci, ya ƙoshi,Ya kuma sha jininsu, ya ƙoshi,Gama Ubangiji Allah Mai Rundunazai hallaka maƙiyansa,A arewa, a bakin Kogin Yufiretis.

11. Ku mutanen Masar, ku haura zuwaGileyadDon ku samo ganye!A banza kuke morar magunguna,Ba za ku warke ba.

12. Kunyarku ta kai cikin sauranal'umma,Kukanku kuma ya cika duniya.Soja na faɗuwa bisa kan soja.Dukansu biyu sun faɗi tare.

13. Ubangiji ya yi magana da Irmiya a kan zuwan Nebukadnezzar, Sarkin Babila, don ya yi yaƙi da ƙasar Masar.

14. “Ku yi shelarsa cikin garuruwanMasar,Cikin Migdol, da Memfis, daTafanes,Ku ce, ‘Ku tsaya, ku yi shiri,Gama takobi yana cin waɗanda sukekewaye da ku!’

15. Me ya sa gunkinka, Afis, ya fāɗi,Wato bijimi, gunkinka bai tsaya ba?Domin Ubangiji ya tunkuɗe shiƙasa!

16. Sun yi ta fāɗuwa,Suna faɗuwa a kan juna,Sai suka ce, ‘Mu tashi mu komawurin mutanenmu,Zuwa ƙasar haihuwarmu, mu gududaga takobin azzalumi!’

17. “Ku ba Fir'auna Sarkin Masarsabon suna,‘Mai yawan surutu, wanda bai rifcizarafi ba!’

18. Ni wanda sunana Ubangiji MaiRunduna Sarki ne,Na rantse da raina, wani zai ɓullo,Kamar Tabor a cikin tsaunuka,Ko kuwa kamar Karmel a bakinteku.

19. Ya ku mazaunan Masar,Ku shirya kayanku don zuwa bauta,Gama Memfis za ta lalace, ta zamakufai,Ba mai zama a ciki.

20. “Masar kyakkyawar karsana ce,Amma bobuwa daga arewa ta aukarmata!

21. Sojojin ijararta kamar 'yan maruƙane, masu yawan kitse,Sun ba da baya, sun gudu, ba sutsaya ba,Domin ranar masifarsu ta zo,Lokacin halakarsu ya yi.

Irm 46