Irm 38:10-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Sa'an nan sarki ya umarci Ebedmelek, mutumin Habasha, ya tafi da mutum talatin su tsamo annabi Irmiya daga cikin rijiyar kafin ya mutu.

11. Sai Ebed-melek ya tafi da mutanen, ya kuma tafi gidan sarki, a É—akin ajiya, ya kwaso tsummoki da tsofaffin tufafi, ya zurara wa Irmiya a rijiyar.

12. Ebedmelek, mutumin Habasha, ya ce wa Irmiya ya sa tsummokin da tsofaffin tufafin a hammatarsa, ya zarga igiya, Irmiya kuwa ya yi yadda aka ce masa.

Irm 38