Irm 38:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Shefatiya ɗan Mattan, da Gedaliya ɗan Fashur, da Yehukal ɗan Shelemiya, da Fashur ɗan Malkiya, suka ji maganar da Irmiya yake faɗa wa dukan mutane cewa,

2. “Ubangiji ya ce wanda ya zauna a wannan birni zai mutu da takobi, da yunwa, da annoba, amma wanda ya fita ya je wurin Kaldiyawa zai rayu, zai sami ransa kamar ganimar yaƙi.

3. Gama Ubangiji ya ce, hakika za a ba da wannan birni a hannun rundunar sojojin Sarkin Babila su ci shi.”

4. Sarakunan suka ce wa sarki, “A kashe mutumin nan, gama yana karya zuciyar sojojin da suka ragu a birnin, da zuciyar sauran jama'a duka ta wurin irin maganganun da yake faɗa musu. Gama wannan mutum ba ya neman jin daɗin zaman wannan jama'a sai dai wahala yake nemar musu.”

5. Sarki Zadakiya ya ce, “Ai, ga shi nan a hannunku, gama sarki ba zai yi abin da ba ku so ba.”

6. Sai suka ɗauki Irmiya suka saka shi a rijiyar Malkiya ɗan sarki, wadda take gidan waƙafi. Suka zurara Irmiya a ciki da igiya. Ba ruwa a rijiyar, sai dai lāka, Irmiya ya nutse cikin lākar.

7. Ebed-melek, bābā, mutumin Habasha, wanda yake a gidan sarki, ya ji labari sun saka Irmiya a rijiya. A lokacin nan, sarki yana zaune a Ƙofar Biliyaminu.

8. Sai Ebed-melek ya fita, ya tafi gaban sarki, ya ce masa,

Irm 38