1. A lokacin da Yehoyakim, ɗan Yosiya yake mulkin Yahuza, sai Ubangiji ya ce wa Irmiya,
2. “Ka tafi gidan Rekabawa, ka yi magana da su, ka kawo su a Haikalin Ubangiji, cikin ɗayan ɗakunan, sa'an nan ka ba su ruwan inabi su sha.”
3. Sai na ɗauki Yazaniya ɗan Irmiya, ɗan Habazziniya, da 'yan'uwansa, da dukan 'ya'yansa maza da dukan iyalin gidan Rekabawa.
4. Na kawo su cikin Haikalin Ubangiji, a ɗakin 'ya'yan Hanan da Igdaliya, mutumin Allah. Ɗakin yana kusa da na shugabanni, a kan ɗakin Ma'aseya ɗan Shallum mai tsaron bakin ƙofa.