Na kawo su cikin Haikalin Ubangiji, a ɗakin 'ya'yan Hanan da Igdaliya, mutumin Allah. Ɗakin yana kusa da na shugabanni, a kan ɗakin Ma'aseya ɗan Shallum mai tsaron bakin ƙofa.