1. A lokacin da Yehoyakim, ɗan Yosiya yake mulkin Yahuza, sai Ubangiji ya ce wa Irmiya,
2. “Ka tafi gidan Rekabawa, ka yi magana da su, ka kawo su a Haikalin Ubangiji, cikin ɗayan ɗakunan, sa'an nan ka ba su ruwan inabi su sha.”
3. Sai na ɗauki Yazaniya ɗan Irmiya, ɗan Habazziniya, da 'yan'uwansa, da dukan 'ya'yansa maza da dukan iyalin gidan Rekabawa.
4. Na kawo su cikin Haikalin Ubangiji, a ɗakin 'ya'yan Hanan da Igdaliya, mutumin Allah. Ɗakin yana kusa da na shugabanni, a kan ɗakin Ma'aseya ɗan Shallum mai tsaron bakin ƙofa.
5. Sa'an nan na sa tuluna cike da ruwan inabi, da ƙoƙuna a gaban Rekabawa, sai na ce musu, “Ku sha ruwan inabi!”
6. Sai suka amsa, suka ce, “Ba za mu sha ruwan inabi ba, gama Yonadab ɗan Rekab, kakanmu, ya umarce mu cewa, ‘Ko ku, ko 'ya'yanku, ba za ku sha ruwan inabi ba har abada,
7. ba kuma za ku gina ɗaki ba, ba kuwa za ku yi shuka ba, ba za ku yi dashe ba, ba za ku yi gonar inabi ba. Za ku zaune cikin alfarwai dukan kwanakin ranku, domin ku yi tsawon rai a ƙasar baƙuncinku.’
8. Mu kuma muka yi biyayya da umarnin da Yonadab ɗan Rekab, kakanmu, ya yi mana, cewa kada mu sha ruwan inabi, mu da matanmu, da 'ya'yanmu mata da maza,
9. kada kuma mu gina wa kanmu gidajen zama. Ba mu da gonar inabi, ko gona ko iri.
10. Amma a alfarwai muke zamanmu. Mun yi biyayya da dukan abin da Yonadab kakanmu ya umarce mu.
11. Amma sa'ad da Nebukadnezzar Sarkin Babila ya kawo yaƙi a ƙasar, sai muka ce, ‘Bari mu tafi Urushalima domin muna jin tsoron sojojin Kaldiyawa da Suriyawa.’ Shi ya sa muke zaune a Urushalima.”
12. Sa'an nan Ubangiji ya yi magana da Irmiya ya ce,