2. A lokacin nan kuwa sojojin Sarkin Babila sun kewaye Urushalima da yaƙi, annabi Irmiya kuwa yana a tsare a gidan waƙafi, a fādar Sarkin Yahuza.
3. Zadakiya Sarkin Yahuza, ya sa shi a kurkuku, gama ya ce, “Don me kake yin annabci? Ka ce, Ubangiji ya ce, ga shi, zai ba da wannan birni a hannun Sarkin Babila, zai kuwa cinye shi da yaƙi.
4. Zadakiya Sarkin Yahuza kuwa, ba zai tsere wa Kaldiyawa ba, amma za a ba da shi a hannun Sarkin Babila. Zai yi magana da shi fuska da fuska, ya kuma gan shi ido da ido.
5. Sarkin Babila kuwa zai tafi da Zadakiya zuwa Babila. Zai zauna can sai lokacin da na ziyarce shi. Ko da ya yi yaƙi da Kaldiyawa ba zai yi nasara ba.”
6. Irmiya ya ce, “Ubangiji ya yi magana da ni, cewa
7. ga shi, Hanamel, ɗan Shallum kawuna, zai zo wurina ya ce mini, ‘Ka sayi gonata wadda take a Anatot, gama kai ne ka cancanci ka fanshe ta, sai ka saye ta.’ ”