33. Amma wannan shi ne alkawarin da zan yi da mutanen Isra'ila bayan waɗancan kwanaki, ni Ubangiji na faɗa. Zan sa dokokina a cikinsu, zan rubuta su a zukatansu, zan zama Allahnsu, su kuma za su zama jama'ata.
34. Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa, ko ɗan'uwansa cewa, ‘Ka san Ubangiji’ ba, gama su duka za su san ni, tun daga ƙarami har zuwa babba. Zan gafarta musu laifofinsu, ba kuwa zan ƙara tunawa da zunubansu ba.”
35. Haka Ubangiji ya ce,Shi wanda ya ba da rana ta haskakayini,Ya sa wata da taurari su ba da haskeda dare,Shi ne yakan dama teku, ya saraƙumanta su yi ruri,Sunansa Ubangiji Mai Runduna.
36. “Idan dai wannan kafaffiyar ka'idata daina aiki a gabana,Ni Ubangiji na faɗa,To, ashe, zuriyar Isra'ila za ta dainazama al'umma a gabana ke nanhar abada.
37. Idan a iya auna sammai a kuma iyabincike tushen duniya a ƙarƙas,To, ashe, zan watsar da dukanzuriyar Isra'ila ke nan sabodadukan abin da suka yi,Ni Ubangiji na faɗa.
38. “Ga shi, kwanaki suna zuwa da za a sāke gina birnin domin Ubangiji, ni Ubangiji na faɗa, tun daga hasumiyar Hananel zuwa yamma, har zuwa Ƙofar Kan Kusurwa.
39. Sa'an nan ma'aunin zai daɗa gaba, har ya kai tudun Gareb, sa'an nan ya nausa zuwa Gowa.
40. Dukan filin kwarin gawawwaki da toka, da dukan filaye har zuwa rafin Kidron zuwa kan kusurwar Ƙofar Doki wajen gabas, za su zama mai tsarki ga Ubangiji. Ba za a ƙara tumɓuke shi ko a rushe shi ba har abada.”