2. A ɗaya kwandon akwai ɓaure masu kyau, kamar nunan fari. A ɗayan kuwa marasa kyau ne, ba mai iya cinsu.
3. Sai Ubangiji ya ce mini, “Irmiya, me ka gani?”Sai na ce, “'Ya'yan ɓaure, akwai masu kyau ƙwarai, akwai kuma marasa kyau ƙwarai, har da ba za su ciwu ba.”
4. Sa'an nan Ubangiji ya ce mini,
5. “Haka ni Ubangiji Allah na Isra'ila na ce, kamar kyawawan ɓauren nan, haka nake ganin mutanen Yahuza waɗanda aka kai su bautar talala a ƙasar Kaldiyawa.
6. Zan lura da su da kyau, in kuma komo da su a wannan ƙasa. Zan gina su, ba zan rushe su ba. Zan kafa su, ba zan tumɓuke su ba.