Irm 22:23-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Ya ku mazaunan Lebanon,Waɗanda suke zaune cikin itatuwanal'ul,Irin nishin da za ku yi sa'ad da azabata same ku,Azaba ce irin ta mace mainaƙuda!

24. “Ni Ubangiji na rantse da raina, ko da Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, zoben hatimi ne a yatsan hannun damana, duk da haka zan kwaɓe shi,

25. in bashe shi a hannun waɗanda suke neman ransa, da a hannun wanda yake jin tsoronsa, wato Nebukadnezzar, Sarkin Babila, da Kaldiyawa.

26. Zan jefar da shi da uwarsa a wata ƙasa inda ba a haife shi ba, a can zai mutu.

27. Amma ƙasan nan da suke marmarin komowa cikinta, ba za su koma cikinta ba.”

28. Ashe, Yekoniya kamar fasasshentulu yake,Wanda ba wanda ya kula da shi?Me ya sa aka watsar da shi da'ya'yansa,A ƙasar da ba su sani ba?

29. Ya ke ƙasa, ƙasa, ƙasa!Ki ji maganar Ubangiji!

30. Haka Ubangiji ya ce,“Rubuta wannan mutum, marar'ya'ya.Mutumin da ba zai yi albarka a dukkwanakinsa ba.Gama ba wani daga zuriyarsaDa zai gāji gadon sarautar Dawuda,Ko ya yi mulki kuma a Yahuza.”

Irm 22