Irm 12:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya Ubangiji, kai adali ne sa'ad da na kawo ƙara a gare ka.Duk da haka zan bayyana ƙarata agabanka,Me ya sa mugaye suke arziki cikinharkarsu?Me ya sa dukan maciya amana sukezaman lafiya,Suna kuwa ci gaba?

2. Kai ka dasa su, sun kuwa yi saiwa,Suna girma, suna kuma ba da'ya'ya,Sunanka na a cikin bakinsu, ammakana nesa da zuciyarsu.

3. Amma kai, ya Ubangiji, kana sane dani, kana ganina,Kai kanka kake gwada tunanina.Ka jawo su kamar tumaki zuwamayanka,Ka ware su domin ranar yanka.

4. Sai yaushe ƙasar za ta dainamakoki,Ciyawar kowace saura kuma ta dainayin yaushi?Saboda muguntar mazaunan ƙasarne dabbobi da tsuntsaye sukaƙare,Domin mutanen suna cewa, “Ba zaiga ƙarshenmu ba.”

Irm 12