Irm 11:20-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Amma ya Ubangiji Mai Runduna,mai shari'ar adalci,Kakan gwada zuciya da tunani,Ka yarda mini in ga sakayyar da zaka yi mini a kansu,Gama a gare ka na danƙamaganata.

21. Saboda haka ga abin da Ubangiji ya faɗa a kan mutanen Anatot, waɗanda suke neman ranka, da suka ce, “Kada ka yi annabci da sunan Ubangiji, in ba haka ba, da hannunmu za mu kashe ka.”

22. Domin haka ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Ga shi kuwa, zan hukunta su, za a kashe samarinsu da takobi, 'ya'yansu mata da maza, yunwa za ta kashe su.

23. Ba wanda zai ragu daga cikin mutanen Anatot, gama zan kawo wa mutanen Anatot masifa, a shekarar hukuncinsu.”

Irm 11