Saboda haka ga abin da Ubangiji ya faɗa a kan mutanen Anatot, waɗanda suke neman ranka, da suka ce, “Kada ka yi annabci da sunan Ubangiji, in ba haka ba, da hannunmu za mu kashe ka.”