Far 39:8-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Amma ya ƙi, ya kuwa faɗa wa matar maigidansa, ya ce, “Ga shi, tun da maigida ya same ni, maigidana ba ruwansa da kome na cikin gida, ya kuwa riga ya sa dukan abin da yake da shi cikin hannuna.

9. Bai fi ni iko cikin gidan nan ba, ba kuma abin da ya hana mini sai ke kaɗai, domin ke matarsa ce. Ƙaƙa fa zan aikata wannan babbar mugunta, in yi wa Allah zunubi?”

10. Ko da yake ta yi ta yi wa Yusufu magana yau da gobe, amma bai biye mata ya kwana da ita ko su zauna tare ba.

11. Amma wata rana, sa'ad da ya shiga cikin gida ya yi aikinsa, mazajen gidan kuma ba wanda yake gidan,

12. sai ta kama rigarsa, tana cewa, “Ka kwana da ni.” Amma ya bar rigarsa a hannunta ya gudu ya fita.

13. Da ta ga ya bar rigarsa a hannunta ya gudu, ya fita waje,

14. sai ta yi kira ga mutanen gidan, ta ce musu, “Ku duba ku gani, ya kawo mana Ba'ibrane ya ci mutuncinmu. Ya zo wurina don ya kwana da ni, sai na yi ihu da ƙarfi.

15. Da ya ji na ta da murya na yi ihu, ya kuwa gudu ya bar rigarsa, ya fita waje.”

16. Ta ajiye rigar a wurinta har maigidansa ya komo.

17. Sai ta mayar masa da magana, ta ce, “Baran nan, Ba'ibrane wanda ka kawo cikinmu, ya shigo wurina don ya ci mutuncina,

18. amma nan da nan da na ta da murya na yi ihu, sai ya gudu ya bar rigarsa a hannuna, ya gudu zuwa waje.”

19. Sa'ad da maigidan Yusufu ya ji abin da matarsa ta faɗa masa, “Ka ji yadda baranka ya yi da ni ke nan,” sai ya husata.

20. Maigidan Yusufu ya ɗauke shi ya māka shi a kurkuku, inda 'yan sarƙa na sarki suke tsare, can ya zauna a kurkuku.

21. Amma Ubangiji yana tare da Yusufu, ya kuwa nuna masa madawwamiyar ƙauna, ya sa ya sami farin jini a wurin yarin kurkukun.

22. Yarin kurkuku ya shugabantar da Yusufu bisa dukan 'yan sarƙa da suke a kurkuku, dukan abin da ake yi a wurin kuma shi yake yi.

23. Yarin kurkukun, ba ruwansa da dukan abin da Yusufu yake kula da shi, domin Ubangiji yana tare da shi, dukan abin da ya yi kuwa Ubangiji yakan sa wa abin albarka.

Far 39