51. Ga Rifkatu nan gabanka, ka ɗauke ta ku tafi, ta zama matar ɗan maigidanka, bisa ga faɗar Ubangiji.”
52. Sa'ad da baran Ibrahim ya ji wannan, ya sunkuyar da kansa ƙasa, ya yi sujada a gaban Ubangiji.
53. Sai baran ya kawo kayan ado na azurfa, da na zinariya, da tufafi, ya bai wa Rifkatu, ya kuma ba ɗan'uwanta da mahaifiyarta kayan ado masu tsada.
54. Shi da mutanen da suke tare da shi suka ci suka sha, suka kwana wurin. Da suka tashi da safe, sai ya ce, “A sallame ni, in koma wurin maigidana.”
55. Ɗan'uwanta da mahaifiyarta suka ce, “Ka bar budurwar tare da mu har ɗan lokaci, kada ya gaza kwana goma, bayan wannan ta tafi.”
56. Amma ya ce musu, “Kada ku makarar da ni, tun da yake Allah ya arzuta tafiyata, a sallame ni domin in koma wurin maigidana.”
57. Suka ce, “Za mu kira budurwar mu tambaye ta.”
58. Suka kirawo Rifkatu suka ce mata, “Za ki tafi tare da wannan mutum?”Sai ta ce, “Zan tafi.”
59. Suka kuwa sallami Rifkatu 'yar'uwarsu da uwar goyonta, da baran Ibrahim da mutanensa.
60. Suka sa wa Rifkatu albarka, suka ce mata,“'Yar'uwarmu, ki zama mahaifiyardubbai,Har dubbai goma,Bari zuriyarki kuma su gāji ƙofofinmaƙiyansu!”
61. Sai Rifkatu da kuyanginta suka tashi suka hau raƙuman, suka bi mutumin. Haka nan kuwa baran ya ɗauki Rifkatu ya koma.
62. A lokacin kuwa Ishaku ya riga ya zo daga Biyer-lahai-royi yana zaune a Negeb.
63. A gabatowar maraice, sai Ishaku ya fita saura ya yi tunani, ya ɗaga idanunsa ya duba, ya ga raƙuma suna zuwa.
64. Da Rifkatu ta ɗaga idanunta, ta hangi Ishaku, sai ta sauka daga raƙumi,
65. ta ce wa baran, “Wane ne mutumin can da yake zuwa daga saura garin ya tarye mu?”Sai baran ya ce, “Ai, maigidana ne.” Ta ɗauki mayafinta ta yi lulluɓi.
66. Sai baran ya faɗa wa Ishaku dukan abin da ya yi.
67. Ishaku kuwa ya shiga da ita cikin alfarwarsa ya ɗauki Rifkatu ta zama matarsa, ya kuwa ƙaunace ta. Ta haka Ishaku ya ta'azantu bayan rasuwar mahaifiyarsa.