Ezra 4:14-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Da yake muke cin moriyar fāda, ba daidai ba ne mu bari a raina sarki. Saboda haka muke sanar da sarki,

15. domin a bincika a littattafan tarihin kakanninka. Za ka gani a littattafan tarihi, cewa wannan birni na tayarwa ne, mai yin ta'adi ga sarakuna da larduna. A nan ne aka ta da hargitsi a dā. Shi ya sa aka lalatar da shi.

16. Muna sanar da sarki fa, idan aka sāke gina wannan birni da garunsa, ba za ka sami abin mallaka a lardin Yammacin Kogi ba.”

17. Sarki kuma ya aika musu da amsa ya ce, “Gaisuwa zuwa ga Rehum shugaban sojoji, da Shimshai magatakarda, da abokansu waɗanda suke zaune a Samariya da lardin Yammacin Kogi.

18. “An karanta mini wasiƙar da kuka aiko mana, filla filla.

19. Na ba da umarni, aka bincika, aka kuwa tarar, cewa wannan birni ya tayar wa sarakuna a dā, an yi tawaye da hargitsi cikinsa.

20. Manya manyan sarakuna sun yi sarauta a Urushalima, waɗanda suka yi mulki a kan dukan lardin Yammacin Kogi, waɗanda aka biya su haraji, da kuɗin shiga da fita na kaya, da kuɗin fito.

21. Saboda haka sai ka umarci waɗannan mutane su daina gina birnin nan, sai lokacin da na ba da umarni.

22. Ka kula fa, kada ka yi kasala a wannan al'amari, don me ɓarna za ta bunƙasa har ta cuci sarki?”

23. Sa'ad da aka karanta wa Rehum, da Shamshai magatakarda, da abokansu, wasiƙar sarki Artashate, suka hanzarta suka tafi wurin Yahudawa a Urushalima, suka gwada musu iko, suka tilasta musu su daina ginin.

24. An tsai da aikin Haikalin Allah a Urushalima, sai a shekara ta biyu ta sarautar Dariyus Sarkin Farisa.

Ezra 4