63. Sai mai mulki ya ce ba za su ci abinci mafi tsarki ba, sai firist ya shawarci Urim da Tummim tukuna, wato kamar kuri'a ke nan.
64-67. Yawan taron jama'a su dubu arba'in da biyu da ɗari uku da sittin (42,360).Barorinsu maza da mata, dubu bakwai da ɗari uku da talatin da bakwai (7,337)Mawaƙa ɗari biyu mata da mazaDawakansu ɗari bakwai da talatin da shidaAlfadaransu ɗari biyu da arba'in da biyarRaƙumansu kuma ɗari huɗu da talatin da biyar neJakunansu kuwa dubu shida da ɗari bakwai da ashirin (6,720)
68. Waɗansu shugabannin gidajen kakanninsu, sa'ad da suka isa Haikalin Ubangiji a Urushalima, sai suka bayar da kyautai da yardar rai don a sāke gina Haikalin Ubangiji a wurin da yake dā.
69. Gwargwadon arzikinsu suka ba da darik dubu sittin da dubu ɗaya (61,000) na zinariya, da maina dubu biyar (5,000) na azurfa, da tufafin firistoci guda ɗari.
70. Firistoci, da Lawiyawa, da waɗansu mutanen da suke zaune a Urushalima da kewayenta, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofi, da ma'aikatan Haikalin, da dukan mutanen Isra'ila suka zauna a garuruwansu.