9. Sai dukan mutanen Yahuza da na Biliyaminu, suka hallara a Urushalima kafin kwana uku, a ran ashirin ga watan tara. Mutanen suka zauna a dandalin Haikali, suna rawar jiki saboda al'amarin, da kuma saboda babban ruwan sama.
10. Ezra firist kuwa ya miƙe tsaye ya ce wa jama'a, “Kun yi rashin aminci, kun auri mata baƙi, ta haka kuka ƙara zunubin Isra'ila.
11. Yanzu sai ku hurta wa Ubangiji Allah na kakanninku, laifinku, ku kuma aikata nufinsa. Ku ware kanku daga mutanen ƙasar da mata baƙi.”
12. Dukan taron jama'a suka amsa da babbar murya, suka ce, “Haka nan ne, haka nan ne, dole ne mu yi yadda ka faɗa.
13. Amma mutane suna da yawa, a lokacin kuwa ana marka, ba za mu iya tsayawa a fili ba, aikin nan kuma ba na kwana ɗaya, ko biyu ba ne, gama mun yi laifi sosai wajen wannan al'amari.
14. Bari shugabanninmu su wakilci dukan taron jama'a, bari kuma dukan waɗanda suke garuruwanmu da suka auri mata baƙi su zo a ƙayyadadden lokaci tare da dattawa da alƙalan garuruwansu, har lokacin da Allah ya huce daga fushinsa a kanmu saboda al'amarin nan.”
15. Jonatan ɗan Asahel da Yazeya ɗan Tikwa ne kaɗai ba su yarda da wannan ba, Meshullam da Shabbetai suka goyi bayansu.
16. Waɗanda suka komo daga zaman talala kuwa suka yi haka. Sai Ezra firist ya zaɓi mutanen da suke shugabannin gidajen kakanninsu. Aka rubuta sunan kowa. Sai suka taru ran ɗaya ga watan goma, don su bincika al'amarin.
17. Suka gama binciken dukan mutanen da suka auri mata baƙi ran ɗaya ga watan fari.