9. Sa'an nan su mazaunan biranen Isra'ila za su tattara makaman mutane, wato garkuwoyi, da bakuna, da kibau da kulake, da māsu, su yi ta hura wuta da su, har ya kai shekara bakwai.
10. Ba za su yi wahalar zuwa jeji don nemo itacen wuta ba, gama za su yi ta hura wuta da makaman. Za su washe waɗanda suka washe su a dā, ni Ubangiji na faɗa.
11. “A wannan rana zan ba Gog makabarta a Isra'ila, a kwarin matafiya a gabashin teku. Makabartar za ta kashe hanyar matafiya, gama a can za a binne Gog da dukan rundunar da take tare da shi. Za a kira wurin Hamongog, wato Kwarin Rundunar Gog.
12. Jama'ar Isra'ila za su yi wata bakwai suna binne su don su tsabtace ƙasar.
13. Dukan jama'ar ƙasar za su yi aikin binnewar, zai zama daraja a gare su a ranar da zan bayyana ɗaukakata, ni Ubangiji Allah na faɗa.
14. A ƙarshen wata bakwai ɗin za su keɓe waɗansu mutane domin su bi ko'ina cikin ƙasar, su binne sauran gawawwakin da suka ragu a ƙasar don su tsabtace ta.