9. Sa'an nan Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum, ka yi annabci a kan iska, ka ce mata, ni Ubangiji Allah na ce ta zo daga kusurwa huɗu, ta hura a kan waɗannan matattu domin su rayu.”
10. Na kuwa yi annabci kamar yadda aka umarce ni, sai numfashi ya shiga cikinsu, suka rayu, suka tashi, suka tsaya da ƙafafunsu. Sun zama babbar runduna ƙwarai.
11. Sa'an nan Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum waɗannan ƙasusuwa su ne mutanen Isra'ila duka. Ga shi, suna cewa, ‘Ƙasusuwa sun bushe, zuciyarmu kuwa ta karai, an share mu ƙaƙaf.’
12. “Domin haka ka yi annabci ka ce musu, ni Ubangiji Allah na ce zan buɗe kaburburansu, in tashe su daga cikin kaburburansu. Zan kuma komar da su gida zuwa ƙasar Isra'ila.
13. Mutanena za su sani ni ne Ubangiji sa'ad da na buɗe kaburburansu na tashe su daga cikinsu.
14. Zan sa Ruhuna a cikinsu za su kuwa rayu. Zan sa su a ƙasarsu sa'an nan za su sani ni Ubangiji na faɗa, na kuwa aikata.”
15. Ubangiji ya kuma yi magana da ni, ya ce,
16. “Ɗan mutum, ka ɗauki sanda, ka rubuta a kansa, ‘Domin Yahuza da magoyan bayansa.’ Ka kuma ɗauki wani sanda, ka rubuta a kansa, ‘Domin Yusufu, sandan Ifraimu, da dukan mutanen Isra'ila, magoyan bayansa.’
17. Ka haɗa su su zama sanda guda a hannunka.
18. Sa'ad da kuma jama'arka suka ce maka ka nuna musu abin da kake nufi da waɗannan,
19. sai ka faɗa musu, cewa ni Ubangiji Allah na ce zan karɓe sandan Yusufu, wanda yake a hannun Ifraimu da mutanen Isra'ila magoyan bayansa, in haɗa shi da sandan Yahuza in maishe su sanda guda a hannuna.
20. “Sa'ad da sandunan da ka yi rubutu a kansu suna hannunka a gabansu,
21. sai ka faɗa musu, cewa ni Ubangiji Allah na ce, zan komo da jama'ar Isra'ila daga wurin al'ummai inda suka warwatsu, zan tattaro su daga ko'ina, in maido su ƙasarsu.
22. Zan maishe su al'umma guda a ƙasar Isra'ila. Sarki ɗaya zai sarauce su duka, ba za su ƙara zama al'umma biyu ba, ba kuwa za su ƙara zama masarauta biyu ba.