Ez 20:12-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Na kuma ba su ranar Asabar don ta zama alama tsakanina da su, don kuma su sani ni ne Ubangiji wanda yake tsarkake su.

13. Amma mutanen Isra'ila suka tayar mini a cikin jeji, ba su bi dokokina da ka'idodina ba, waɗanda idan mutum ya kiyaye su, zai rayu. Suka ɓata ranar Asabar ƙwarai. Sai na ce zan zubo musu da hasalata, in aukar da fushina a kansu.

14. Amma saboda sunana ban yi wannan ba, domin kada a saɓi sunana a cikin sauran al'umma waɗanda a kan idonsu na fisshe su.

15. Na kuma rantse musu a cikin jeji, cewa ba zan kai su ƙasar da na ba su ba, ƙasar da take cike da yalwar albarka, wato ƙasar da take mafi albarka duka,

16. domin sun ƙi su bi ka'idodina da dokokina. Suka ɓata ranar Asabar ɗina, gama zuciyarsu ta fi so ta bauta wa gumaka.

17. “Duk da haka na yafe musu, ban hallaka su ba, ban kuma shafe su a jeji ba.

18. Sai na ce wa 'ya'yansu a jeji, ‘Kada ku bi dokokin ubanninku, ko kuwa ku kiyaye ka'idodinsu, kada kuma ku ɓata kanku da gumakansu.

Ez 20