Dan 6:21-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Sai Daniyel ya ce wa sarki, “Ran sarki ya daɗe!

22. Allahna ya aiko mala'ikansa ya rufe bakunan zakoki, ba su iya yi mini lahani ba, domin ban yi wa Allah laifi ba, ban kuma yi maka ba.”

23. Sarki ya cika da murna ƙwarai, ya umarta a fito da Daniyel daga kogon. Sai aka fito da Daniyel daga kogon, aka ga ba wani lahani a jikinsa saboda ya dogara ga Allahnsa.

24. Sai sarki ya umarta a kawo mutanen nan da suka yi wa Daniyel maƙarƙashiya, a tura su, da 'ya'yansu, da matansu cikin kogon zakoki. Tun ba su kai ƙurewar kogon ba, sai zakoki suka hallaka su, suka kakkarye ƙasusuwansu gutsi-gutsi.

25. Dariyus sarki kuwa ya rubuta wa dukan jama'a da al'ummai, waɗanda suke zaune a duniya duka, ya ce, “Salama ta yalwata a gare ku.

26. Ina umartar mutanen da suke cikin mulkina su yi rawar jiki, su ji tsoron Allah na Daniyel,Gama shi Allah ne mai rai, Madawwami,Sarautarsa ba ta tuɓuwa,Mulkinsa kuma madawwami ne.

27. Yakan yi ceto, yakan kuma kuɓutar,Yana aikata alamu da mu'ujizai a sama da duniya.Shi ne wanda ya ceci Daniyel daga bakin zakoki.”

28. Daniyel kuwa ya bunƙasa a zamanin mulkin Dariyus da na Sairus mutumin Farisa.

Dan 6