39. A bayanka kuma za a yi wani mulki wanda bai kai kamar naka ba. Za a yi wani mulki kuma na uku mai darajar tagulla, wanda zai mallaki dukan duniya.
40. Za a kuma yi mulki na huɗu, mai ƙarfi kamar baƙin ƙarfe. Da yake baƙin ƙarfe yakan kakkarya, ya ragargaje abubuwa, haka nan wannan mulki zai ragargaje sauran mulkoki.
41. Ka kuma ga an yi ƙafafun da yatsotsin da baƙin ƙarfe gauraye da yumɓu, wato mulkin zai rabu, amma zai kasance da ƙarfi kamar na baƙin karfen da yake gauraye da yumɓu.
42. Kamar yadda yatsotsin ƙafafun rabi baƙin ƙarfe, rabi kuma yumɓu ne, haka nan mulkin zai kasance, rabi da ƙarfi, rabi kuma da gautsi.
43. Kamar yadda ka ga baƙin ƙarfen ya gauraya da yumɓun, haka nan mulkokin za su gauraye da juna ta wurin aurayya, amma ba za su haɗu da juna ba, kamar yadda baƙin ƙarfe da yumɓu ba su haɗuwa.
44. A kwanakin waɗannan sarakuna, Allah na Sama zai kafa wani mulki wanda ba zai taɓa rushewa ba har abada, ba kuma za a gādar da shi ga waɗansu mutane ba. Wannan mulki zai ragargaje dukan waɗannan mulkoki, ya kawo ƙarshensu. Wannan mulki zai dawwama har abada.
45. Kamar yadda ka ga an gutsuro dutse ba da hannun ɗan adam ba, ya kuwa ragargaje baƙin ƙarfen, da tagullar, da yumɓun, da azurfar, da zinariyar, Allah Maɗaukaki ya sanar wa sarki abin da zai faru nan gaba. Mafarkin tabbatacce ne, fassarar kuma gaskiya ce.”
46. Sarki Nebukadnezzar kuwa ya fāɗi a gaban Daniyel, ya gaishe shi, sa'an nan ya umarta a miƙa hadaya, da hadaya ta turare ga Daniyel.
47. Ya kuma ce wa Daniyel, “Hakika, Allahnka, Allahn alloli ne da Ubangijin sarakuna, mai bayyana asirai, gama ka iya bayyana wannan asiri.”
48. Sai sarki ya ba Daniyel girma mai yawa, da manya manyan kyautai masu yawa. Ya kuma naɗa shi mai mulki bisa dukan lardin Babila. Ya shugabantar da shi bisa dukan masu hikima waɗanda suke Babila.
49. Daniyel kuwa ya roƙi sarki ya naɗa Shadrak, da Meshak, da Abed-nego su zama masu kula da harkokin lardin Babila, amma Daniyel yana fādar sarki.