1. “A wannan lokaci Mika'ilu babban shugaba wanda yake lura da jama'arka zai bayyana. A lokacin za a yi tashin hankali irin wanda ba a taɓa yi ba, tun da aka yi duniya. Amma a lokacin za a ceci jama'arka waɗanda aka rubuta sunayensu cikin littafi.
2. Waɗanda suka rasu za su tashi, waɗansu zuwa rai madawwami, waɗansu kuwa zuwa kunya da madawwamin ƙasƙanci.
3. Waɗanda suke da hikima za su haskaka kamar sararin sama, waɗanda kuma suka juyar da mutane da yawa zuwa adalci, za su zama kamar taurari har abada abadin.
4. “Amma kai, Daniyel, sai ka rufe maganar, ka kuma kulle littafin, har zuwa ƙarshen lokaci. Mutane da yawa za su yi ta kai da kawowa, ilimi kuma zai ƙaru.”
5. Sa'an nan ni Daniyel na duba, sai ga waɗansu biyu a tsaye, ɗaya a wannan gāɓa ɗayan kuma a waccan gāɓar kogin.
6. Dayansu ya ce wa mutumin da yake sāye da rigar lilin, wanda yake tsaye a gaɓar kogin, “Sai yaushe waɗannan abubuwan banmamaki za su ƙare?”