Amos 5:13-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Ashe, ba abin mamaki ba ne,Da masu hankali suka kame bakinsuA waɗannan kwanaki na mugunta.

14. Ku yi ƙoƙari, ku yi nagarta, bamugunta ba,Domin ku tsira.Sa'an nan ne Ubangiji AllahMaɗaukakiZai kasance tare da ku sosai,Kamar yadda kuka ɗauka!

15. Ku ƙi mugunta, ku ƙaunacinagarta,Ku yi adalci cikin majalisaralƙalanku!Watakila Ubangiji Allah MaiRundunaZai yi wa sauran da suka ragu nawannan al'umma alheri.

16. Haka Ubangiji Allah Mai Rundunaya ce,“Za a yi kuka, a yi kururuwa atitunan birninku saboda azaba.Daga ƙauyuka za a kirawomutaneSu zo su yi makokin.Waɗanda suka mutu, tare da masumakoki da aka ijarar da su.

17. Za a yi kuka ko'ina cikin dukangonakin inabinkuGama zan zo in yi muku horo.”

18. Taku ta ƙare, ku da kuke marmarinzuwan ranan nan ta Ubangiji!Wane amfani wannan rana za ta yimuku?Rana ta baƙin ciki ce,Ba ta murna ba.

19. Zai zama kamar wanda ya tsere wazakiYa fāɗa a bakin beyar!Ko kuwa kamar wanda ya komogida,Ya dāfa bango, maciji ya sare shi.

20. Ranar Ubangiji za ta kawo baƙinciki,Ba murna ba.Rana ce ta damuwa ba ta fara'a ba.

21. Ubangiji ya ce,“Na ƙi bukukuwanku na addini.Ina ƙyamarsu!

22. Sa'ad da kuka kawo mini hadayunƙonawaDa hadayunku na tsaba, ba zankarɓa ba.Ba kuma zan karɓi turkakkundabbobinkuWaɗanda kuka miƙa mini hadayungodiya ba.

23. Ku yi shiru da yawan hargowarwaƙoƙinku.Ba na so in saurari kaɗe-kaɗenku dabushe-bushenku.

24. Sai ku sa adalci da nagarta su gudanoa yalwaceKamar kogin da ba ya ƙafewa.

25. “Ya ku, jama'ar Isra'ila, ai, a waɗannan shekaru arba'in da kuka yi cikin jeji kuka kawo mini sadaka da hadayu,

26. duk da haka, kuka ɗauki siffofin gumakanku na taurari, wato Sakkut da Kaiwan, waɗanda kuka yi wa kanku.

27. Ni kuwa zan sa ku yi ƙaura zuwa wata ƙasa gaba da Dimashƙu.” Ubangiji, Allah Mai Runduna, shi ne ya faɗa.

Amos 5