A.m. 9:14-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Ga shi kuma manyan firistoci sun ba shi izini ya ɗaure duk mai yin addu'a da sunan har a nan ma.”

15. Amma Ubangiji ya ce masa, “Kai dai, je ka, domin shi ma'aikacina ne zaɓaɓɓe, domin yă sanar da sunana ga al'ummai, da sarakuna, da kuma Isra'ilawa.

16. Domin zan sanar da shi yawan wuyar da lalle zai sha saboda sunana.”

17. Sai Hananiya ya tafi, ya shiga gidan. Da ya ɗora masa hannu, ya ce, “Ya ɗan'uwana Shawulu, Ubangiji ne ya aiko ni, wato Yesu, wanda ya bayyana a gare ka a kan hanyar da ka biyo, domin ka sāke gani, a kuma cika ka da Ruhu Mai Tsarki.”

18. Nan take sai wani abu kamar ɓawo ya faɗo daga idanunsa, sai ya sāke gani. Sa'an nan ya tashi, aka yi masa baftisma.

19. Sai ya ci abinci, ƙarfinsa kuma ya komo.Shawulu kuwa ya yi 'yan kwanaki tare da masu bi da suke Dimashƙu.

20. Nan da nan ya fara wa'azin Yesu a majami'unsu, cewa shi ne Ɗan Allah.

21. Duk waɗanda suka ji shi, suka yi ta al'ajabi, suka ce, “Ashe, ba wannan ne ya watsa masu yin addu'a da sunan nan a Urushalima ba? Ya zo nan ne ma da niyyar ya kai su gaban manyan firistoci a ɗaure.”

22. Sai Shawulu ya ƙara ƙarfafa, yana ta dama hankalin Yahudawan da suke zaune a Dimashƙu, yana tabbatarwa, cewa Yesu shi ne Almasihu.

23. Bayan an ɗan daɗe Yahudawa suka ƙulla shawara su kashe shi.

24. Amma Shawulu ya sami labarin makircinsu. Dare da rana suna fako a ƙofofin gari don su kashe shi,

25. amma da daddare almajiransa suka tafi da shi, suka zura shi ta wata taga a jikin garu cikin babban kwando.

A.m. 9