3. Sa'an nan Sulemanu da dukan waɗanda suke tare da shi, suka tafi masujadar da take a Gibeyon, gama alfarwar sujada ta Allah, wadda Musa, bawan Ubangiji ya yi a jeji, tana can.
4. Amma dai Dawuda ya riga ya ɗauko akwatin alkawari na Allah daga Kiriyat-yeyarim, ya kawo shi a wurin da ya shirya, gama ya kafa masa alfarwa a Urushalima.
5. Amma bagaden tagulla wanda Bezalel ɗan Uri daga dangin Hur, ya yi, yana a gaban Wuri Mai Tsarki na Ubangiji, sai Sulemanu da taron jama'a suka yi sujada ga Ubangiji a can.
6. Sulemanu kuwa ya haura, ya tafi wurin da bagaden tagulla yake a gaban Ubangiji, a cikin alfarwa ta sujada, ya miƙa hadayun ƙonawa dubu a kansa.
7. A wannan dare Allah ya bayyana ga Sulemanu, ya ce masa, “Ka roƙe ni abin da kake so in ba ka.”
8. Sai Sulemanu ya ce wa Allah, “Ka nuna wa tsohona Dawuda madawwamiyar ƙaunarka, har ka naɗa ni sarki a matsayinsa.
9. Yanzu fa ya Ubangiji Allah, alkawarin da ka yi wa tsohona ya cika, gama ka naɗa ni sarki a kan jama'a mai yawa kamar turɓaya.
10. Yanzu sai ka ba ni hikima da sani yadda zan iya kai da kawowa a gaban wannan jama'a, gama wa zai iya mulkin wannan jama'a taka mai yawa haka?”
11. Allah kuwa ya amsa wa Sulemanu ya ce, “Tun da kana da irin wannan tunani a zuciyarka, ba ka kuwa roƙi dukiya, ko wadata, ko girma, ko ran maƙiyanka ba, ba ka kuma roƙi tsawon rai ba, amma ka roƙa wa kanka hikima da sani domin ka iya yin mulkin jama'ata wadda na naɗa ka sarki a kanta,
12. to, na ba ka hikima da sani. Zan kuma ba ka dukiya, da wadata, da girma, waɗanda ba wani sarkin da ya taɓa samun irinsu, ba kuma wani sarkin da zai taɓa samun irinsu.”