16. Elisha kuwa ya ce mata, “Baɗi war haka za ki rungumi ɗa na kanki.”Sai ta ce, “A'a, ya shugabana, mutumin Allah, kada fa ka yi mini ƙarya.”
17. Amma macen ta sami juna biyu, ta kuwa haifi ɗa a daidai lokacin da Elisha ya faɗa mata.
18. Da yaron ya yi girma, sai wata rana ya bi mahaifinsa gona zuwa wurin masu girbi.
19. Sai ya ce wa mahaifinsa, “Wayyo, kaina, kaina.”Uban kuwa ya ce wa baransa, “Ka ɗauke shi, ka kai shi wurin uwar.”
20. Da aka ɗauke shi, aka kai wa uwar, sai ya zauna a cinyar uwar har rana tsaka, sa'an nan ya rasu.
21. Sai ta hau, ta kwantar da shi a gadon annabi Elisha, sa'an nan ta rufe ƙofa, ta fita.
22. Sa'an nan ta aika a faɗa wa mijinta, ta ce, “Ka aiko mini ɗaya daga cikin barori da jaki domin in tafi wurin annabi Elisha, zan komo da sauri.”
23. Sai ya ce, “Me ya sa za ki tafi wurinsa yau? Ai, yau ba amaryar wata ba ce, ba kuwa ranar Asabar ba ce.”Ita kuwa ta ce, “Ba kome, kada ka damu.”
24. Amma ta yi wa jakin shimfiɗa, ta kuma ce wa baranta, “Yi ta kora mini jakin, kada ka sassauta, sai na faɗa maka.”
25. Sai ta kama hanya, ta tafi wurin annabi Elisha a Dutsen Karmel.Sa'ad da annabi Elisha ya gan ta zuwa, sai ya ce wa Gehazi, wato baransa, “Duba, ga Bashunemiya can.
26. Ruga ka tarye ta, ka tambayi lafiyarta, da ta mijinta, da ta ɗanta.”Ta amsa, ta ce, “Lafiya ƙalau.”
27. Sa'ad da ta isa wurin annabi Elisha a kan dutsen, sai ta kama ƙafafunsa. Sai Gehazi ya zo zai ture ta. Amma mutumin Allah ya ce masa, “Ƙyale ta kurum, gama tana da baƙin ciki ƙwarai, Ubangiji kuwa ya ɓoye mini abin.”
28. Matar ta ce masa, “Na roƙe ka ka ba ni ɗa ne? Ashe, ban ce maka kada ka ruɗe ni ba?”
29. Elisha ya ce wa Gehazi, “Yi ɗamara, ka ɗauki sandana ka tafi. Duk wanda ka gamu da shi, kada ka gaishe shi, duk kuma wanda ya gaishe ka kada ka amsa, ka tafi ka ɗora sandana a fuskar yaron.”
30. Sai macen ta ce, “Na rantse da Ubangiji da kai kuma, ba zan bar ka ba.” Sai Elisha ya tashi, ya bi ta.
31. Gehazi kuma ya yi gaba, ya ɗora sandan a fuskar yaron, amma ba motsi ko alamar rai. Saboda haka ya koma, ya taryi Elisha, ya faɗa masa yaron bai farka ba.
32. Da Elisha ya kai ɗakin, ya ga yaron yana kwance matacce a gadonsa.
33. Sai ya shiga ya rufe ƙofa, daga shi sai yaron, ya yi addu'a ga Ubangiji.