2 Sar 24:6-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Yehoyakim ya rasu. Ɗansa Yekoniya ya gāji gadon sarautarsa.

7. Sarkin Masar kuma bai sāke fitowa daga Masar ba, gama Sarkin Babila ya ƙwace dukan ƙasar da take ta Sarkin Masar, tun daga rafin Masar har zuwa Kogin Yufiretis.

8. Yekoniya yana da shekara goma sha takwas sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki wata uku a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Nehushta 'yar Elnatan, mutumin Urushalima.

9. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji kamar yadda tsohonsa ya yi.

10. A zamaninsa ne sojojin Nebukadnezzar Sarkin Babila suka zo Urushalima, suka kewaye ta da yaƙi.

11. Nebukadnezzar ya zo birnin lokacin da sojojinsa suka kewaye birnin da yaƙi.

2 Sar 24