1. A shekara ta biyu ta sarautar Yehowash ɗan Yehowahaz Sarkin Isra'ila, Amaziya ɗan Yowash Sarkin Yahuza ya ci sarauta.
2. Yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki shekara ashirin da tara a Urushalima. Sunan tsohuwarsa kuwa Yehowaddin ta Urushalima.
3. Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji, amma bai kai kamar kakansa Dawuda ba. Ya yi kamar yadda tsohonsa, Yowash ya yi.
4. Amma ba a kawar da wuraren yin tsafi a tuddai ba. Mutane suka yi ta miƙa hadaya, da ƙona turare a matsafai na kan tuddai.
5. Sa'ad da mulkin ya kahu sosai a hannun Amaziya, sai ya kashe fādawan da suka kashe tsohonsa.
6. Amma bai kashe 'ya'yan masu kisankai ɗin ba, don ya bi abin da aka rubuta a littafin dokokin Musa, inda Ubangiji ya umarta cewa, “Kada a kashe iyaye saboda 'ya'ya, kada kuma a kashe 'ya'ya saboda iyaye, amma kowa zai mutu saboda laifin kansa.”
7. Ya kuma kashe Edomawa dubu goma (10,000) a Kwarin Gishiri, sa'an nan ya ƙwace Sela, ya ba ta suna Yokteyel, haka ake kiranta har wa yau.
8. Amaziya kuwa ya aiki manzanni wurin Yehowash, ɗan Yehowahaz, ɗan Yehu, Sarkin Isra'ila, yana nemansa da yaƙi.
9. Yehowash Sarkin Isra'ila ya mayar wa Amaziya Sarkin Yahuza da amsa cewa, “A dutsen Lebanon ƙaya ta aika wurin itacen al'ul ta ce, ‘Ka ba ɗana 'yarka ya aura.’ Sai mugun naman jeji na Lebanon ya wuce, ya tattake ƙayar.
10. Yanzu kai, Amaziya, ka bugi Edomawa don haka zuciyarka ta kumbura. To ka gode da darajar da ka samu, ka tsaya a gida, gama don me kake tonon rikici da zai jawo maka fāduwa, kai da mutanen Yahuza?”
11. Amma Amaziya bai ji ba. Sai Yehowash Sarkin Isra'ila ya tafi, ya shiga yaƙi da Amaziya, Sarkin Yahuza a Bet-shemesh ta Yahuza.
12. Mutanen Isra'ila suka ci na Yahuza. Sai kowane mutum ya gudu gida.