2 Sar 11:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'ad da Ataliya, uwar Ahaziya, ta ga ɗanta ya rasu, sai ta tashi ta hallaka dukan 'ya'yan sarauta.

2. Amma Yehosheba 'yar sarki Yoram, 'yar'uwar Ahaziya, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya daga cikin 'ya'yan sarki waɗanda aka kashe, ta ɓoye shi da mai renonsa, an yi ta renonsa cikin ɗaki. Da haka ta tserar da shi daga Ataliya, har ba a kashe shi ba.

3. Ya zauna tare da ita shekara shida a ɓoye, a cikin Haikalin Ubangiji sa'ad da Ataliya take mulkin ƙasar.

4. A shekara ta bakwai sai Yehoyada ya aika ya kawo shugabannin Keretiyawa da na masu tsaro a Haikalin Ubangiji. Ya yi alkawari da su, ya sa suka yi rantsuwa a Haikalin Ubangiji, sa'an nan ya nuna musu ɗan sarki.

5. Ya kuma umarce su cewa, “Abin da za ku yi ke nan, sai sulusinku da sukan zo aiki a ranar Asabar, su yi tsaron gidan sarki.

6. Sulusinku kuma zai kasance a ƙofar Sur. Ɗaya sulusin kuma zai kasance a bayan masu tsaro, haka za ku yi tsaron gidan, ku tsare shi.

7. Ƙungiyarku biyu kuma waɗanda sukan tashi aiki ran Asabar, za su yi tsaron Haikalin Ubangiji da kuma sarki.

8. Za ku kewaye sarki, kowane mutum ya riƙe makaminsa. Duk wanda ya yi ƙoƙari ya zo kusa, sai a kashe shi. Sai ku kasance tare da sarki duk lokacin da zai fita da duk lokacin da zai shiga.”

9. Shugabannin fa suka aikata bisa ga dukan abin da Yehoyada firist ya umarta. Kowa ya zo duk da mutanensa waɗanda za su huta aiki ran Asabar tare da waɗanda za su yi aiki ran Asabar, suka zo wurin Yehoyada.

10. Firist kuwa ya ba shugabannin māsu da garkuwoyin Dawuda waɗanda suke cikin Haikalin Ubangiji.

11. Matsara suka tsaya, kowa da makaminsa a hannu, daga wajen kudu na Haikalin zuwa wajen arewa. Suka kewaye bagade da Haikali.

12. Sa'an nan ya fito da ɗan sarki, ya sa kambin sarauta a kansa, ya kuma ba shi dokokin. Suka naɗa shi, suka zuba masa man naɗawa, sa'an nan suka yi tāfi suna cewa, “Ran sarki ya daɗe.”

13. Da Ataliya ta ji muryoyin matsara da na jama'a, sai ta zo wurin mutane a Haikalin Ubangiji.

2 Sar 11