6. Abner ya ƙasaita sosai a gidan Saul a lokacin da ake yaƙi tsakanin jarumawan Saul da na Dawuda.
7. Saul yana da ƙwarƙwara mai suna Rizfa, 'yar Aiya. Sai Ish-boshet ya ce wa Abner, “Me ya sa ka kwana da ƙwarƙwarar tsohona?”
8. Abner ya husata saboda wannan magana, ya ce, “Kana zato ni maci amanar ƙasa ne? Kana tsammani ina wa ƙasar Yahuza aiki ne? Tun da farko ina ta nuna alheri ga gidan Saul, tsohonka, da 'yan'uwansa, da abokansa, ban kuwa ba da ka a hannun Dawuda ba. Amma ga shi, yau ka zarge ni da laifin kwartanci game da wannan mata.
9. Allah ya la'anta ni, idan ban yi wa Dawuda abin da Ubangiji ya rantse masa ba,
10. wato in mayar wa Dawuda da sarautar gidan Saul. In kafa kursiyin Dawuda a kan Isra'ila da kan Yahuza tun daga Dan har zuwa Biyer-sheba.”
11. Ish-boshet kuwa bai ce wa Abner uffan ba, don yana jin tsoronsa.
12. Sai Abner ya aiki manzanni zuwa wurin Dawuda a Hebron, ya ce, “Ƙasar ta wane ne? Ka yi mini alkawari, ni kuwa zan goyi bayanka, in sa dukkan Isra'ilawa su bi ka.”
13. Dawuda ya ce, “Da kyau, zan yi maka alkawari a kan wannan sharaɗi, ba za ka ga fuskata ba sai ka kawo mini matata, Mikal, 'yar Saul, sa'ad da za ka zo wurina.”
14. Sa'an nan Dawuda ya aiki manzanni zuwa wurin Ish-boshet, ɗan Saul, ya ce, “Ka ba ni matata, Mikal, wadda na biya sadakinta da loɓa ɗari ta Filistiyawa.”
15. Sai Ish-boshet ya aika aka ƙwato Mikal daga wurin mijinta, Falti, ɗan Layish.
16. Mijinta ya bi ta yana ta kuka har zuwa Bahurim. Sai Abner ya ce masa ya koma, ya kuwa koma.
17. Abner ya shawarci dattawan Isra'ila, ya ce, “Dā ma can kuna so Dawuda ya sarauce ku.
18. To, yanzu sai ku yarda ya sarauce ku, gama Ubangiji ya yi wa Dawuda alkawari ya ce, ‘Ta hannun bawana, Dawuda, zan ceci jama'ar Isra'ila daga hannun Filistiyawa, da na dukan abokan gābansu.’ ”
19. Abner kuma ya yi magana da mutanen Biliyaminu, sa'an nan ya tafi ya faɗa wa Dawuda a Hebron abin da dukan Isra'ilawa da dukan kabilar Biliyaminu suka ga ya yi kyau, su yi.
20. Abner tare da mutum ashirin suka zo wurin Dawuda a Hebron, Dawuda kuwa ya yi musu liyafa.
21. Sai Abner ya ce wa Dawuda, “Zan tashi in tafi in tattara wa ubangijina sarki dukan Isra'ilawa, domin su yi alkawari da kai, kai kuma ka sarauce su yadda kake so.” Dawuda kuwa ya sallami Abner, ya tafi lafiya.
22. Sai ga barorin Dawuda da Yowab sun komo daga hari. Sun kawo ganima mai yawa. Abner kuwa ya riga ya tafi, gama Dawuda ya riga ya sallame shi, ya tafi lafiya.
23. Da Yowab da sojojin da suke tare da shi suka iso, sai aka faɗa masa cewa, “Abner ɗan Ner ya zo wurin sarki, sarki kuwa ya bar shi ya tafi lafiya.”
24. Sai Yowab ya tafi wurin sarki ya ce, “Me ke nan ka yi? Abner ya zo wurinka, me ya sa ka bar shi ya tafi lafiya?
25. Ka sani Abner ɗan Ner ya zo ya ruɗe ka ne, ya san fitarka da shigarka, ya kuma san dukan abin da kake yi.”