22. Sai ga barorin Dawuda da Yowab sun komo daga hari. Sun kawo ganima mai yawa. Abner kuwa ya riga ya tafi, gama Dawuda ya riga ya sallame shi, ya tafi lafiya.
23. Da Yowab da sojojin da suke tare da shi suka iso, sai aka faɗa masa cewa, “Abner ɗan Ner ya zo wurin sarki, sarki kuwa ya bar shi ya tafi lafiya.”
24. Sai Yowab ya tafi wurin sarki ya ce, “Me ke nan ka yi? Abner ya zo wurinka, me ya sa ka bar shi ya tafi lafiya?
25. Ka sani Abner ɗan Ner ya zo ya ruɗe ka ne, ya san fitarka da shigarka, ya kuma san dukan abin da kake yi.”
26. Da Yowab ya fita daga wurin Dawuda, sai ya aiki manzanni su bi bayan Abner. Suka komo da shi a rijiyar Sira, amma Dawuda bai sani ba.
27. Sa'ad da Abner ya komo Hebron, sai Yowab ya raɓa da shi wajen ƙofar garin kamar zai gana da shi, sai ya soke shi a ruwan ciki, ya fāɗi ya mutu, saboda alhakin jinin ɗan'uwansa, Asahel.
28. Daga baya sa'ad da Dawuda ya ji, sai ya ce, “Ni da mulkina baratattu ne a gaban Ubangiji daga alhakin jinin Abner ɗan Ner har abada.
29. Allah ya sa alhakin jinin ya faɗa kan Yowab da dukan gidan ubansa. Ya sa kada a rasa mai ɗiga, ko kuturu, ko wanda yake dogara sanda, ko wanda aka kashe da takobi, ko wanda ba shi da abinci, a gidan Yowab.”
30. Ta haka Yowab da ɗan'uwansa Abishai suka kashe Abner saboda ya kashe ƙanensu, Asahel, a wurin yaƙi a Gibeyon.
31. Dawuda kuwa ya ce wa Yowab da dukan mutanen da suke tare da shi, “Ku kyakketa tufafinku, ku sa tsummoki, ku yi makoki domin Abner.” Sarki Dawuda kuwa ya bi bayan makara.
32. Suka binne Abner a Hebron. Sarki ya ta da murya ya yi kuka a kabarin Abner. Dukan mutane kuma suka yi kuka.
33. Sarki ya yi wannan makoki domin Abner, ya ce,“Don me Abner zai mutu kamar wawa?
34. Hannuwansa ba a ɗaure suke ba,Ƙafafunsa kuma ba a dabaibaye suke ba.Ya mutu kamar wanda mugayen mutane suka kashe.”Dukan mutane suka yi kuka kuma saboda shi.
35. Mutane kuwa suka zo su ba Dawuda magana, ko ya ci abinci tun rana ba ta faɗi ba. Amma Dawuda ya rantse ya ce, “Allah ya buge ni in mutu nan, idan na ɗanɗana abinci ko wani abu kafin rana ta faɗi.”
36. Da mutanen suka lura, sai suka yarda da abin da sarki ya yi, suka kuma ji daɗin kowane abu da sarki ya yi.
37. A wannan rana dukan mutanen Dawuda da dukan mutanen Isra'ila suka gane, ashe, ba nufin Dawuda ba ne a kashe Abner ɗan Ner.
38. Sarki ya ce wa fādawansa, “Ba ku sani ba, basarake ne, babban mutum ne kuma ya faɗi a cikin Isra'ila yau?