Da Yowab ya fita daga wurin Dawuda, sai ya aiki manzanni su bi bayan Abner. Suka komo da shi a rijiyar Sira, amma Dawuda bai sani ba.