Sa'ad da Abner ya komo Hebron, sai Yowab ya raɓa da shi wajen ƙofar garin kamar zai gana da shi, sai ya soke shi a ruwan ciki, ya fāɗi ya mutu, saboda alhakin jinin ɗan'uwansa, Asahel.