2 Sam 2:10-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Ish-boshet, ɗan Saul, yana da shekara arba'in sa'ad da ya ci sarautar Isra'ila, ya yi shekara biyu yana sarauta. Amma mutanen Yahuza suka bi Dawuda.

11. Dawuda ya yi shekara bakwai da rabi yana sarautar Yahuza a Hebron.

12. Abner, ɗan Ner, tare da fādawan Ish-boshet, ɗan Saul, suka tashi daga Mahanayim zuwa Gibeyon.

13. Sai kuma Yowab, ɗan Zeruya, tare da fādawan Dawuda suka fita suka tafi tarye su a tafkin Gibeyon. Suka zauna, waɗannan a wannan gefe, waɗancan a wancan gefe na tafkin.

14. Sai Abner ya ce wa Yowab, “Bari samarin su tashi su yi kokawa a gabanmu.”Yowab kuwa ya ce, “To, sai su tashi.”

15. Sai suka tashi, suka haye. Mutum goma sha biyu a madadin mutanen Biliyaminu da Ish-boshet, ɗan Saul, mutum goma sha biyu kuma a madadin mutanen Dawuda.

16. Kowa ya kama abokin kokawarsa a kā, suka soki juna a kwiɓi da takuba. Suka faɗi tare. Aka sa wa wurin suna Helkat-hazzurim, wato filin takuba, wurin yana nan a Gibeyon.

17. Yaƙin kuwa ya yi zafi a ranar. Mutanen Dawuda suka ci Abner da mutanen Isra'ila.

18. 'Ya'yan Zeruya, maza, su uku suna nan, wato Yowab, da Abishai, da Asahel. Asahel maguji ne kamar barewa.

19. Sai ya tasar wa bin Abner haiƙan, bai kauce ba.

20. Da Abner ya waiga, sai ya ce, “Kai ne Asahel?”Ya amsa, “Ni ne.”

21. Abner ya ce masa, “Ka daina haye mini, ka runtumi ɗaya daga cikin samarin, ka kama shi, ka karɓe masa makaminsa.” Amma Asahel bai daina binsa ba.

22. Abner kuma ya sāke ce masa, “Ka daina bina, kada ka sa in kashe ka fa! Idan na kashe ka kuwa, yaya zan yi ido biyu da dan'uwanka, Yowab?”

23. Amma Asahel bai daina binsa ba, Abner dai ya nashe shi da gindin māshi a ciki, sai mashin ya fita ta bayansa. Ya fāɗi ya mutu nan take. Duk wanda ya zo inda Asahel ya fāɗi ya mutu, sai ya tsaya cik.

24. Amma Yowab da Abishai suka bi Abner, har faɗuwar rana, suka isa tudun Amma, wanda yake gaban Gaiya, a hanya zuwa jejin Gibeyon.

2 Sam 2